11 Satumba 2021 - 11:54
​Lebanon: An Kafa Sabuwar Gwamnati Karkashin Shugabancin Miqati

Bayan kwashe tsawon fiye da shekara guda ana ta kai ruwa rana, a jiya an kafa sabuwar gwamnati a kasar Lebanon, karkashin shugabancin Najib Miqati.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, a jiya Juma’a an kafa sabuwar majalisar ministoci a kasar Lebanon, wadda tsohon Firayi ministan kasar Najib Miqati zai jagoranta.

An sanar da kafa sabuwar gwamnatin ne bayan kammala tattaunawa tsakanin shugaban kasar ta Lebanon Michael Oun da kuma shugaban majalisar dokoki Nabih Birri, gami da shugaban sabuwar gwamnati Najib Miqati a jiya a fadar shugaban kasar ta Lebanon a birnin Beirut.

A jawabin da ya gabar jim kadan bayan amincewa da gwamnatinsa, Najib Miqati ya bayyana cewa, gwamnatin da ya kafa gwamnati ce ta kwararru, ba gwamnati ce ta bangaranci da ko kabilanci ko akida ta addini ba.

Ya ce ya san akwai jan aiki a gabansa, amma kuma abu ne mai yiwuwa a iya cimma abubuwa da daman a ci gaba matukar dai aka zage dantse aka sa himma kan hakan, inda ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta yi da kowace kasa ta duniya in ban da Isra’ila.

Sannan kuma ya yi alkawalin gudanar da zaben ‘yan majalisar dokoki da na kananan hukumomi a ranar 8 ga watan Mayun shekara mai zuwa kamar yadda aka tsara.

Tun daga ranar 4 ga watan Agustan shekarar da ta gabata ce dai gwamnatin Hassan Diyab ta sanar da yin murabus, biyo bayan tarwatsewar wasu abubuwa masu karfi da aka samu tashar jiragen ruwa ta birnin Beirut.

Daga lokacin ne kuma shugaban kasar Lebanon umarci Mustafa Adib day a kafa sabuwar gwamnati, amma aranar 26 ga watan Satumban 2020 ya gabatar da uzurinsa.

Bayan nan kuma an umarci Saad Hariri da ya kafa sabuwar gwamnati, wanda shi ma bayan kwashe tsawon watanni 9 ba tare da ya iya kafa gwamnati ba, a cikin watan Yulin wannan shekara ya gabatar da uzurinsa kan hakan, wanda kuma daga lokacin ne aka umarci Najib Miqati da ya kafa sabuwar gwamnati a kasar Lebanon.

342/